Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo Da Blair Sun Cimma Daidaiton Ra'ayi A Kan Zimbabwe - 2002-02-07


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya da Firayim Minista Tony Blair na Britaniya wanda ke ziyara a Abuja, sun cimma ra'ayi guda kan bukatar dake akwai ta gudanar da zaben shugaban kasa tsakani da Allah cikin wata mai zuwa a Zimbabwe.

A wurin taron 'yan jarida yau a babban birnin Nijeriya, Abuja, Mr. Obasanjo ya ce ya shaidawa shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe irin bukatar dake akwai ta kawo karshen fitinar siyasa, tare da kyale 'yan kallo da 'yan jaridan kasashen waje su sa idanu kan yadda za a gudanar da zaben.

Shugaban na Nijeriya ya ce idan ba haka aka yi ba kuwa, Afirka da sauran duniya ba zasu amince da sakamakon zaben ba.

A nasa bangaren, Firayim Minista Blair ya amince da bukatar gudanar da zaben tsakani da Allah, yana mai cewa tilas a kyale 'yan kallon kasa da kasa da kuma 'yan jaridar kasashen waje suje su kasar ta Afirka domin ganin yadda za a gudanar da zaben. Britaniya tana sahun gaba cikin masu sukar lamirin matakan shugaba Mugabe na murkushe abokan adawar siyasa da kafofin yada labarai kafin zaben na watan Maris.

XS
SM
MD
LG