Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakil Ahmed Muttawakil -Takaitaccen Tarihinsa - 2002-02-09


Tsohon ministan harkokin wajen 'yan Taleban, Wakil Ahmed Muttawakil, na hannun daman shugaban Afghanistan Mullah Mohammad Omar ne a lokacin da suka yi mulki, amma kuma ana daukarsa a zaman daya daga cikin masu sassaucin ra'ayi a cikin kungiyar Taleban.

Mullah Muttawakil matashi ne, an ce shekarunsa na haihuwa kimanin Talatin ne. Shi dan kabilar Pashtun ne, kuma mahaifinsa shaihin malamin addini ne. An haife shi a kusa da Kandahar. An bada rahoton cewar yayi karatu a wata makarantar addini dake Pakistan. Yana ji tare da yin magana a harshen larabci, yana kuma jin Turanci.

Mullah Muttawakil ya zamo aminin Mullah Omar, inda ya fara zamowa direbansa, da tafintarsa, ya kuma zamo kakakinsa.

Amma kuma an ce bai so matakin da Taleban ta dauka a watan Maris na bara ba, na rushe manya-manyan gumakan tarihi na Buddha a Bamiyan.

Rahotannin kafofin labarai sun kuma ce Mullah Muttawakil bai amince da kawancen kut da kut da Taleban ta kulla da kungiyar ta'addanci ta al-Qa'ida ba. An ambaci majiyoyin tsaro suna fadin cewa Mullah Muttawakil ya bata da maigidansa Mullah Omar a karshen shekarar da ta shige saboda sabanin ra'ayi kan yadda Taleban ta ki yarda ta mika shugaban al-Qa'ida, Osama bin Laden ga Amurka.

XS
SM
MD
LG