Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Iran ke Bukin Cika Shekaru 23 da Juyin Juya Halin Islama - 2002-02-11


Yayinda yake share fagen zanga zangar adawa da Amirka a yau dinnan a birnin Tehran, Shugaban Iran Mohammad Khatami ya baiyana kalaman Shugaba Bush a zaman “wadanda ba su dace da Shugaba ba kuma na zagi.” Shugaban na Iran ya ce a yau da kasar ke bukin cikata shekaru 23 da juyin juya halin Islama za’a bada karfi ne wajen nuna hushi tareda ambaton kalaman maida martani ga Shugaba Bush. A karshen watan Janairu ne Shugaba Bush ya ce Iran, Iraq da Korea ta Arewa su suka hadu suka kafa “kadarkon shedanci” wanda ke marawa aiyukan ta’adanci tareda bidar makaman kare dangi. Haka Amirka ta zargi Iran da neman sanya kafar angulu ga sabuwar gwamnati ta Afghanistan wadda ke da ra’ayin kasashen yamma. Haka kuma, Shugaba Khatami na Iran ya ce ya damu kwarai ganin kudade masu yawa da Shugaba Bush ke nema a kasafin kudin da ya aikewa da majalisar dokokinsa domin neman amincewarsu.

XS
SM
MD
LG