Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Suna Gudu Daga Fada A Liberiya, Yayin da Wani jirgi Ya Fadi a Kasar - 2002-02-15


Jami’an Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun ce dubban mutane na yin tururuwa suna ficewa daga yankunan da ake caba kazamin fada tsakanin ’yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar Laberiya.

Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ta ce a makon da ya gabata, mutane kimanin dubu 15 ne suka nemi mafaka a Monrovia, babban birnin kasar, sannan kuma an tsugunar da wasu mutanen kimanin dubu 30 a cikin sansanonin da aka kafa a cikin karamar hukumar Bong a arewacin birnin Monrovia. Matar da ke magana da yawun hukumar ta MDD a Geneva ta ce fadan ya rutsa da karin wasu dubban mutane, ya jefa su tsaka mai wuya.

A halin yanzu dai an bada labarin cewa dakarun gwamnatin Laberiya da ’yan tawaye suna ci gaba da gwabzawa da juna a kewayen garin Tubmanburg, mai tazarar kimanin kilomita 70 da Monrovia. A makon jiya ne shugaban kasar Laberiya, Charles Taylor, ya ayyana dokar-ta-baci a wani kokarin neman yin maganin ’yan tawayen.

A halin da ake ciki, a yau jumma’a wani jirgin saman sufuri kirar Rasha ya fadi kusa da babban filin jirgin saman Liberia, ya kashe mutum akalla guda.

Jami’an gwamnati a Monrovia, babban birnin kasar, sun ce wannan jirgi kirar Antonov-12, ya nemi iznin saukar gaggawa a lokacin da yake ratsawa ta samaniyar kasar. Jirgin ya fadi yayi bindiga a wani wuri mai tazarar kilomita 6 daga babban filin jirgin saman Roberts International, jim kadan a bayan da aka ba shi iznin sauka.

An tura wasu fasinjoji 9 dake cikin jirgin zuwa asibiti domin a yi musu jinya.

Jami’an gwamnati da na filin jirgin saman ba su bayyana asalin wannan jirgi ko fasinjojinsa, ko inda suka dosa ko kuma abinda suke dauke da shi ba.

XS
SM
MD
LG