Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Pakistan Ta Bada Umurnin Ci Gaba Da Tsare Sheikh Omar - 2002-02-25


Wata Kotu a Pakistan ta bada umarnin a cigaba da tsare mutumin nan dake da hannu wajen sacewa da kuma kashe dan jaridannan, Ba’Amerike, Daniel Pearl, na karin tsawon wasu kwanaki goma sha hudu, yayin da ake cigaba da binciken wannan kisan.

A yau aka bada sanarwar wannan shawara, bayan da Musulmi mai tsatsauran ra’ayin Islama, haifafan kasar Biitaniya, Ahmed Omar Saeed, wanda aka fi sani da sunan Sheik Omar, ya bayyana gaban Kotun dake birnin na Karachi, inda Mr. Pearl ya bace a ran 23 ga watan Janairun daya gabata.

Alkalin wannan Kotun ya dan jinkirta shigar da wannan kara, domin a bai wa masu yin binciken wannan kisan damar samo hujjoji da kuma gawar Mr. Pearl, da za’a yi amfani da su wajen wannan shari'ar.

A tun farkon wannan watan aka kama Sheik Omar, yana kuma tare da hukuma a makon jiya lokacin da aka karbi faifan bidiyon daya nuna yadda aka kashe Mr. Pearl.

XS
SM
MD
LG