Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Karin 'Yan Adawa Biyu Da Laifin Cin Amanar Kasa A Zimbabwe - 2002-02-26


An tuhumi wasu karin jami'an adawa biyu da laifin cin amanar kasa a Zimbabwe, dangane da wata makarkashiyar da aka yi zargin an kitsa, ta kashe shugaba Robert Mugabe. Wannan mataki ya kara zaman tankiya a kasar, ana dab da gudanar da zaben shugaban kasa a wata mai zuwa.

Wani kakakin jam'iyyar adawa ta "Movement for Democratic Change" ya ce 'yan sanda sun tuhumi babban sakataren jam'iyyar, Welshman Ncube, da wani dan majalisar dokoki, Renson Gasela, a bayan da suka kira su domin yi musu tambayoyi.

A jiya litinin, 'yan sanda sun tuhumi shugaban 'yan adawa Morgan Tsvangirai da irin wannan laifin, a saboda zargin da aka yi cewa ya hada baki da wani kamfanin bada shawarwari kan dabarun siyasa dake kasar Canada domin kashe shugaba Mugabe.

Mr. Tsvangirai ya musanta wannan zargi, yana mai fadin cewa an shirya shi ne da nufin hana shi kalubalantar Mr. Mugabe a zaben shugaban kasa na ranakun 9 da 10 ga watan Maris.

An sako jami'an 'yan adawar uku daga wakafi a bayan da aka tuhume su.

A halin da ake ciki, Mr. Tsvangirai ya shaidawa 'yan jarida cewar ana ci gaba da gallazawa magoya bayan 'yan adawa ta hanyar abinda ya kira 'tashin hankalin da ake aikatawa da sunan hukuma.' Amma kuma ya ce 'yan kallon zabe na kasa da kasa sun taimaka wajen kwantar da wutar wasu fitinu.

Amurka, da Britaniya da wasu kasashen sun yi tur da tuhumar cin amanar kasa da aka yi wa Mr. Tsvangirai. A yau talata Australiya tayi barazanar kafawa Zimbabwe takunkumi idan har ba a kyale shugaban 'yan adawar yayi takara a zaben shugaban kasar ba.

XS
SM
MD
LG