Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Gwamnati Da Na 'Yan Adawa Sun Kece Raini A Madagascar - 2002-02-27


An yi arangama a babban birnin Madagascar, tsakanin magoya bayan shugaba Didier Ratsiraka, da na madugun ’yan hamayya Marc Ravalomanana, wanda ya ayyana kansa a zaman halaltaccen shugaban wannan tsibiri dake gabar kudancin Afirka.

Daruruwan ’yan zanga-zanga, dauke da sanduna da duwatsu, sun gwabza da magoya bayan Mr. Ravalomanana, a lokacin wani gangamin goyon bayan gwamnati mafi girma da aka gani cikin makonni da dama.

Mr. Ravalomanana, wanda shi ne magajin garin Antananarivo, babban birnin kasar, ya ayyana kansa a zaman shugaban kasa a makon jiya, matakin da ya sa ita kuma gwamnati ta yanzu ta kafa dokar-ta-baci a kasar. A jiya talata madugun ’yan hamayyar ya fara zaben ’yan majalisar zartaswarsa.

Mr. Ravalomanana ya ki yarda da sakamakon zaben da ya nemi da a gudanar da zagaye na biyu na zaben fitar da gwani tsakaninsa da shugaba Ratsiraka, yana mai cewa an yi magudi a zaben watan Disamba, kuma da ya kamata a ce ya lashe zaben kai tsaye a zagayen farko. Kusan kullum sai magoya bayansa sun yi zanga-zanga tun daga lokacin zaben.

Kasashen duniya sun roki Mr. Ravalomanana da ya yarda ya shiga cikin zagaye na biyu na zaben fitar da gwani a ranar 24 ga watan Maris.

XS
SM
MD
LG