Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankalin Addini Mai Muni Ya Buwayi Yammacin Kasar Indiya - 2002-03-01


Dakarun tsaron kasar Indiya suna zaune cikin shirin ko-ta-kwana a Jihar Gujarat dake yammacin kasar, yayin da ake ci gaba da tashin hankali mai muni na addini, wanda ya zuwa yanzu jami'ai sun ce ya kashe mutane fiye da 250 cikin kwanaki biyu.

Daruruwan sojojin gwamnati suna yin sintiri a titunan Ahmedabad, birni mafi girma a Jihar ta Gujarat, inda aka samu rahotannin kashe-kashe mafi yawa. Wasu 'yan tsageran addinin Hindu, sun cunna wuta a wata unguwar share-ka-zauna ta Musulmi a bayan garin birnin a yau Jumma'a, inda suka hallaka mutane kimanin 30.

A wasu sassan jihar ta Gujarat kuma, an bada rahotannin yin dauki-ba-dadi tsakanin gungu-gungun 'yan Hindu da Musulmi. An kafa dokar hana yawo baki daya a akasarin sassan jihar, yayin da hukumomi suka umurci sojoji da su bude wuta kan duk wanda suka yi ido hudu da shi, a wani yunkurin kawo karshen wannan tashin hankali. An kama mutane fiye da dubu daya tun lokacin da tarzoma ta barke jiya alhamis.

Ministan tsaron Indiya, George Fernandes, yana rangadin wannan jiha mai fama da tarzoma, yana mai kiran da a kawo karshen tashin hankali a wannan wuri inda Musulmi da mabiya addinin Hindu suka jima suna zaman tare da juna.

Tarzoma ta barke a bayan da wasu 'yan tsagera Musulmi suka cunna wuta a wani jirgin kasa dake dauke da 'yan tsageran addinin Hindu a ranar laraba, har mutane 58 suka mutu.

Jami'an tsaro a sauran sassan kasar Indiya sun fara zama cikin damara a bayan da Majalisar Hindu ta Duniya mai tsattsauran ra'ayi tayi kiran da ayi yajin aiki a yau Jumma'a. An bada rahoton arangamomi a birnin Bombay, yayin da wasu 'yan tsageran addinin Hindu dake kokarin tilastawa mutane yin aiki da shirin yajin aiki suka nemi hana zirga-zirgar jiragen kasa.

XS
SM
MD
LG