Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Adawa Na Madagascar Ya Kafa Majalisar Ministoci Kishiyar Ta Gwamnati - 2002-03-01


Madugun 'yan adawa na kasar Madagascar ya bada sanarwar kafa majalisar ministoci kishiyar ta gwamnati, yana mai kara zafafa tankiyar da ake yi kan sakamakon zabe tare da yunkurin cire shugaba Didier Ratsiraka daga kan karagar mulki.

A yau Jumma'a Marc Ravalomanana ya gabatar da 'yan majalisar zartaswarsa su 17 ga 'yan jarida gaban majalisar gudanarwa ta Antananarivo, babban birnin kasar.

A halin da ake ciki, magoya bayansa sun yi zanga-zanga a kan tituna, duk da dokar-ta-bacin da shugaba Ratsiraka ya ayyana jiya alhamis.

Shugaba Ratsiraka ya shaidawa 'yan jarida cewar bada son ransa ya dauki wannan matakin ba sai don saboda yawan yajin aiki da tarzoma mai muni a babban birnin kasar. Ya nada gwamnan soja domin magance wannan lamari ya kuma ce an dorawa rundunar sojoji alhakin maido da zaman lafiya.

Madugun 'yan adawar ya ce shine ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar 16 ga watan Disamba kai tsaye, ya kuma ki yarda ya shiga zaben fitar da gwanin da aka shirya gudanarwa ranar 24 ga watan nan na Maris tsakaninsa da shugaban na yanzu.

A ranar laraba, gwamnati ta kafa dokar hana yawon dare a bayan da 'yan zanga-zanga masu goyon bayan gwamnati suka yi arangama da magoya bayan 'yan adawa a Antananarivo kan sakamakon zaben. Mutane fiye da goma suka ji rauni a arangamar ta ranar laraba.

XS
SM
MD
LG