Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tsagera Sun Hana 'Yan Adawa Yin Gangami a Zimbabwe - 2002-03-01


'Yan tsageran jam'iyyar da take yin mulkin kasar Zimbabwe sun kona tayu suka kafa shingaye kan hanyoyi a garin Marondera, abinda ya tilastawa 'yan adawa soke wani gangamin siyasar da suka shirya na yakin neman zaben shugaban kasar ad za a yi cikin watan nan.

Jami'an jam'iyyar adawa ta MDC sun ce ala tilas shugaban jam'iyyar, Morgan Tsvangirai, ya soke wannan taron siyasa a saboda rashin kwanciyar hankali a garin, mai tazarar kilomita 70 a gabas da Harare, babban birnin kasar.

Jami'an adawa suka ce 'yan sanda da sojoji cikin damara sosai ta yaki, sun kewaye inda aka shirya yin wannan gangami, suka tsorata magoya bayan 'yan adawar. 'Yan adawa sun zargi jami'an tsaron da laifin hada baki da 'yan tsagera na jam'iyyar dake mulkin kasar.

Mr. Tsvangirai shine babban mai kalubalantar shugaba Robert Mugabe a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranakun 9 da 10 ga wannan wata na Maris.

XS
SM
MD
LG