Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ci Gaba Da Yin Ruwan Bam a Tsaunukan Afghanistan - 2002-03-03


Jiragen saman yakin Amurka sun koma ga yin ruwan ban kan wuraren da ake zaton 'yan al-Qa'ida da Taleban sun labe a tsaunukan gabashin Afghanistan, a bayan da sojoji na kasa suka kasa zakulo su duk da kazamin fadan da aka gwabza.

Wannan farmakin soja dake faruwa a kudu da Kabul, babban birnin Afghanistan, shine mafi girma da aka kaddamar tun watan Disamba. An yi imanin cewa akwai askarawan al-Qa'ida da Taleban su kimanin dubu 2 zuwa 5 da suka yi tunga cikin ramukan karkashin duwatsu da kogunan duwatsu na lardin Paktia a wajen garin Gardez.

Fadan ya barke ranar Jumma'a, inda Amurka tayi ta jefa bama-bamai domin kashe kwarin guiwar masu tsaron wuraren. Amma kuma da sojojin Afghanistan da na Amurka su dubu 1 da 500 suka kai farmaki ta kasa a ranar asabar, ba su samu nasarar kutsawa ba.

Wata sanarwar da rundunar sojojin Amurka ta bayar ta ce an kashe sojan Amurka da na Afghanistan uku, yayin da aka raunata wasu sojojin Amurka da na Afghanistan wadanda ba a fadi yawansu ba. ba a san irin barnar da aka yi wa 'yan al-Qa'ida da Taleban ba.

Sanarwar ta ce wannan fada yana yin tsanani a wasu lokuta.

A jiya asabar da maraice, jiragen saman yakin Amurka sun sako wasu sabbin bama-bamai da aka fara kera samfurinsu cikin 'yan kwanakin nan wadanda ke shake mutanen dake cikin wani rami na karkashin kasa ta hanyar tsotse iskar dake cikin ramin.

Pakistan ta ce ta tura sojojinta domin su toshe bakin iyakarta ta arewa maso yammaci da Afghanistan domin hana mayakan Taleban da al-Qa'ida tserewa.

XS
SM
MD
LG