Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbo Jirgin Saman Amurka A Bakin Daga A Afghanistan - 2002-03-04


An harbo wani jirgin saman yakin sojan Amurka mai saukar ungulu a yankin gabashin Afghanistan.

Har yanzu babu cikakken bayanin abinda ya faru. Amma ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce an kashe wasu sojojin Amurka a lokacin da aka harbo wannan jirgi jiya lahadi da daddare.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron ta Amurka, Victoria Clarke, ta ce ba a tabbatar da ko sojoji nawa suka mutu a cikin wannan jirgi da aka harbo ba, haka kuma ba a san yawan wadanda suka mutu ba a lokacin da aka yi ta dauki-ba-dadi da sojojin al-Qa'ida da na Taleban a bayn da jirgin yayi saukar gaggawa a gabashin Afghanistan.

Wannan jirgi yana rufawa sojojin da Amurka ke yiwa jagoranci baya ne a gwabzawar da suke yi gaba da gaba da dakarun al-Qa'ida da na Taleban a kudu da garin Gardez.

Jiragen saman yaki na Amurka suna yin luguden bam kan wuraren da abokan gabarsu suka ja daga, a wani bangare na farmakin da aka kaddamar ranar Jumma'a da maraice.

An tabbatar da kashe sojan Amurka daya da mayakan Afghanistan uku ranar asabar a lokacin da mayakan al-Qa'ida da Taleban suka turje, suka yi kememe a wuri guda.

Jami'an Amurka sun ce mayakan al-Qa'ida da na Taleban da suka rage sun sake taruwa wuri guda a cikin jerin kogunan duwatsu da ramukan karkashin kasa dake kusa da garin Gardez a lardin Paktia. Jami'an Afghanistan a yankin sun ce mayakan sun kai dubbai.

Wannan farmaki shine mafi girma da aka kaddamar a Afghanistan a cikin wannan shekara, kuma ya kunshi sojoji dubu 1 da 500 na Afghanistan, da Amurka da na kasashen kawance. Kasashen kawance da dama suna cikin wannan farmaki cikinsu har da Australiya, da Canada, da Denmark, da Faransa, da Jamus da kuma Norway.

XS
SM
MD
LG