Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'Yan Tawayen Saliyo Ya Gurfana Gaban Kotu... - 2002-03-04


Madugun 'yan tawayen Saliyo, Foday Sankoh, ya bayyana a kotu a Freetown, babban birnin kasar, tare da wasu tsoffin 'yan tawaye su 12, domin su saurari tuhumar da ake yi musu ta kisan kai.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron tuhumar Mr. Sankoh har sai zuwa ranar 11 ga watan maris. Mr. Sankoh bai ce uffan ba game da tuhumar da ake yi masa a zaman na yau.

Ministan shari'a na Saliyo, Solomon Berewa, ya ce madugun kungiyar "Revolutionary United Front" yana iya fuskantar hukumcin kisa idan aka same shi da laifi.

A cikin watan Janairu aka ayyana kawo karshen yakin basasar shekaru 10 a kasar Saliyo.

Ana tsare da Mr. Sankoh ba tare da an tuhume shi ba, a wani wurin da ba a bayyana ba a Freetown, tun lokacin da aka damke shi a tsakiyar shekarar 2000. An kulle shi a bayan da kungiyar 'yan tawayensa ta bijirewa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla, ta bude wuta kan wasu 'yan zanga-zanga, ta kashe kimanin 20.

A ranar Jumma'a shugaba Ahmed Tejan Kabbah ya dage dokar-ta-baci wadda ta bada ikon kamawa da tsare mutane ba tare da tuhuma ba, domin jam'iyyun siyasa su samu sa'idar zagayawa yakin neman zabe na kasa baki daya da za a yi a cikin watan Mayu.

Ministan shari'a Berewa ya ce a saboda dage dokar-ta-bacin, ba za a iya ci gaba da tsare Mr. sankoh da sauran 'yan tawayen ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

An kashe mutane kimanin dubu 200 a mummunan yakin basasar da aka gwabza a kasar Saliyo dake Afirka ta Yamma, sannan kuma da gangan 'yan tawaye suka yi ta yanke hannuwa da kafafuwa da sauran gabobin wasu dubban mutane.

XS
SM
MD
LG