Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankali Yana Karuwa a Isra'ila da Yammacin Kogin Jordan - 2002-03-05


Yawan mutanen dake mutuwa a tashe-tashen hankula tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ya ci gaba da karuwa a yau talata, yayin da aka kai sabbin hare-hare. An kashe 'yan Isra'ila biyar da Falasdinawa uku ya zuwa yanzu a wannan tashin hankali na baya-bayan nan.

Tashin hankali na yau talata ya faro daga lokacin da wani Bafalasdine dan bindiga ya bude wuta cikin wani gidan abinci a Tel Aviv, inda ya kshe 'yan Isra'ila uku.

Sa'o'i a bayan wannan, wani Bafalasdine dan kunar-bakin-wake ya tada bam cikin wata motar safa ya kashe kansa da wani dan Isra'ila a garin Afula dake tsakiyar Isra'ila.

A sauran tashe-tashen hankulan da suka wakana, Falasdinawa 'yan bindiga a yankin Yammacin Kogin Jordan, sun yi kwanton bauna suka abka kan masu wucewa da motoci, inda suka kashe wata mace guda. Wani abu da ya fashe a harabar wata makarantar Larabawa a gabashin birnin Qudus, ya raunata mutane 8 cikinsu har da yara kanana.

Jiragen saman kai farmaki masu saukar ungulu na Isra'ila sun cilla makamai masu linzami kan hedkwatar jami'an tsaron Falasdinawa a Khan Younis dake Zirin Gaza. Ba a samu rahoto na jikkata a wannan harin ba ya zuwa yanzu.

haka kuma, Falasdinawa su akalla 15 sun ji rauni, wasunsu mai muni, a lokacin da wani abu mai karfin gaske yayi bindiga a birnin Gaza.

XS
SM
MD
LG