Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Dake Mulkin Afirka ta Kudu Ta Zargi Jimmy Carter Kan Cutar AIDS - 2002-03-10


Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta zargi tsohon shugaban Amurka, Jimmy carter, da laifin neman yin amfani da 'yan Afirka ta Kudu a zaman "dabbobi na gwaji" a yaki da cutar Kanjamau, ko AIDS.

Mr. Carter, wanda ya ziyarci Afirka ta Kudu a ranar Jumma'a, yayi kira ga gwamnatin kasar da ta kara azamar yaki da cutar kanjamau tare da fadada rarraba magungunan jinyar amsu fama da wannan cuta.

A cikin wata sanarwa, jam'iyyar ANC ta ce Mr. Carter yana da niyyar yina mfani da 'yan Afirka ta Kudu a zaman dabbobin gwaji domin biyan muradun kamfanonin harhada magunguna kawai.

Har ya zuwa yanzu ba a samu tsohon shugaban na Amurka domin jin ta bakinsa ba.

Shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu yayi kokarin takaita yin amfani da wani magani mai suna "Nevirapine" wanda aka ce bincike ya nuna cewar yana rage yadda uwa kan harbi dan tayin cikinta da kwayar cutar HIV mai haddasa cutar kanjamau. Mr. Mbeki ya kalubalanci alakar dake tsakanin kwayar HIV da cutar AIDS.

Afirka ta Kudu ta fi kowace kasa a duniya yawan mutane masu dauke da kwayoyin cutar na HIV da AIDS, inda mutane miliyan biyar daga cikin miliyan 45 da na kasar suke dauke da wannan mummunar kwayar cuta. Waatau kowane mutum daya daga cikin tara a Afirka ta Kudu yana dauke da kwayar cutar.

XS
SM
MD
LG