Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Nijeriya, Afirka ta Kudu da Australiya Suna London Domin Tattauna Batun Zimbabwe - 2002-03-19


A yau talata shugabannin Nijeriya da Afirka ta Kudu da kuma Ausytraliya suke ganawa a London, domin tattauna matakan takunkumin da watakila kungiyar "Commonwealth" zata iya sanyawa kasar Zimbabwe.

Kungiyar ta "Commonwealth" ta nada shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya, da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu da kuma Firayim Minista John Howard na Australiya, domin su nazarci irin matakan da ya kamata a dauka a kan Zimbabwe.

An yi zargin cewa hukumomin Zimbabwe sun yi magudi domin tabbatar da cewa shugaba Robert Mugabe ya samu nasara a wannan zabe.

A jiya litinin, Mr. Obasanjo da Mr. Mbeki sun gana da shugaba Mugabe tare da madugun 'yan adawa Morgan Tsvangirai, a birnin Harare. Ba a bayyana irin abubuwan da aka tattauna ko aka cimma a tattaunawar ba.

A halin da ake ciki, Mr. Tsvangirai ya ce a shirye yake ya gana domin tattaunawa da shugaba Mugabe.

XS
SM
MD
LG