Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya gana da manyan mukarrabai domin sake nazarin matakan tsaro a kasar, a bayan mummunan harin da aka kai ranar lahadi kan wata majami'ar dake kusa da ofishin jakadancin Amurka a birnin Islamabad.
Janar Musharraf ya kirawo manyan jami'an 'yan sanda da gwamnonin lardunan kasar domin ganawar da aka yi yau talata a babban birnin kasar. Matar wani ma'aikacin jakadancin Amurka tare da wata 'yarsu budurwa, suna daga cikin mutane biyar da aka kashe a wannan hari na ranar lahadi.
'Yan sanda sun ce sun yi imanin cewa daya daga cikin mutane biyar din da suka mutu, wanda har yanzu ba a san ko wanene ba, shi ne ya kai harin.
Mutane 45 sun ji rauni a wannan harin da 'yan sanda suke kyautata zaton masu kishin addinin Islama ne suka kai.