Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Sun Shirya Takardar Ayyana Sauye-Sauye - 2002-03-26


Shugabannin Afirka da suke Nijeriya domin taron kolin da za a bude yau talata, sun shirya yin na'am da wata Takardar Ayyanawa da aka tsara da nufin bunkasa ayyukan tattalin arziki da sauye-sauyen siyasa a nahiyar.

Shugabannin da suka hallara a Abuja, babban birnin Nijeriya, suna kirkiro da wani daftarin yin sauye-sauye da ake kira Sabon Kawancen Raya Nahiyar Afirka, ko NEPAD a takaice.

Shugabannin kasashe kimanin 20 zasu tattauna yadda wannan kawance na NEPAD zai janyo jarin dala miliyan dubu 64 kowace shekara daga waje domin farfado da tattalin arzikin kasashen Afirka dake fama da matsaloli. Ana sa ran akasarin wannan kudi na gudanar da shirin zai fito ne daga aljihun masu zuba jari na kasashen yammacin duniya.

Wasu ma'aikatan diplomasiyya sun damu cewar kasashen yammacin duniya, musamman ma Britaniya da Amurka, ba zasu bada goyon bayan kirki ga wannan kawancen bunkasa harkokin tattalin arziki na NEPAD ba a saboda zaben shugaban kasar da aka tabka rikici kansa a Zimbabwe cikin wannan wata. An sake zaben shugaba Robert Mugabe a wannan zaben da kasashen yammaci suka yi tur ad shi a zaman na magudi.

Shugabanni a wajen wannan taron koli na Abuja, zasu kuma takali wasu batutuwan dabam, cikinsu har da zaman lafiya da tsaro, aikin gona da bude kasuwanni, da kuma batun tsara tattalin arziki.

Kasashen da zasu tura shugabanninsu ko manyan kusoshin gwamnati zuwa wurin wannan taron sune: Nijeriya, Senegal, Mali, Afirka ta Kudu, Botswana, Mozambique, kamaru, Jamhuriyar Kwango (Kwango-Brazzaville), Gabon, Habasha, Mauritius, Rwanda, Aljeriya, Tunisiya da Zambiya.

Kasashen Tanzaniya, Uganda, Ghana da Tarayyar Tsibiran Sao Tome da Principe zasu halarci taron a zaman 'yan kallo.

XS
SM
MD
LG