Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama Tayi Tur Da Nijeriya Saboda Kisan Gilla - 2002-04-02


Wata sananniyar kungiyar kare hakkin Bil Adama ta fito da kakkausar harshe tana yin tur da Nijeriya saboda kisan gillar da aka yi wa fararen hula su fiye da 200 a shekarar da ta shige.

A cikin sanarwar da ta bayar jiya litinin, kungiyar "Human Rights Watch" ta ce a watan Oktobar bara, sojojin Nijeriya sun kai wani farmakin da suka tsara shi tsaf kan 'yan kabilar Tiv a Jihar Binuwai. Wannan kisan gilla, wanda wadanda suka kubuta suka bayyana shi dalla-dalla, ramuwar gayya ce ta kashe sojoji 19 da aka yi a yankin makonni biyu kafin nan.

Kungiyar ta ce a lokacin wannan kisan gilla kuma, daruruwan sojoji sun lalata gidaje, da kantuna da sauran gine-gine a garuruwa fiye da bakwai cikin jihar ta Binuwai.

Kungiyar "Human Rights Watch" ta bayyana kashe-kashen a kisa ba tare ad shari'a ba, abinda ya saba kai tsaye da dokokin kare hakkin Bil Adama na duniya. Ta soki gwamnatin Nijeriya saboda rashin fitowa tayi tur da wannan mataki da kakkausar harshe, ko kuma hukumta wadanda suka aikata shi. Rahoton ya ce rashin yin wani abu daga bangaren gwamnati, tamkar karawa sojojin guiwar ci gaba da take hakkin Bil Adama ne.

XS
SM
MD
LG