Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Hanawa Anthony Zinni Ganawa Da Yasser Arafat - 2002-04-04


Isra'ila ta ki yarda da rokon wakilin Amurka a Gabas ta Tsakiya, Anthony Zinni, na ganawa da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a ofishinsa dake Ramallah, a yankin Yammacin kogin Jordan.

Jakadan Amurka a Isra'ila, Daniel Kurtzer, shi yayi wannan rokon a farkon makon nan, amma sai jami'an Isra'ila suka ki yarda, suna masu cewa yana da hadari sosai ga Mr. Zinni yayi tattaki zuwa ofishin Malam Arafat.

Ita ma tawagar kasashen Turai wadda zata doshi Gabas ta Tsakiya a yau alhamis domin kokarin yin sulhun gaggawa, ta matsa a kan lallai sai a kyale ta ta gana da Malam Arafat. Amma kuma jami'an Turai sun ce har yanzu Isra'ila ba ta ba su iznin hakan ba.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce karfin wannan tawaga tata, zai dogara kan ko Isra'ilar zata kyale su gana da shugaban na Falasdinawa da aka killace.

A bayan ganawa da manyan jami'ai, jami'an Kasashen Turai sun ce wakilan nasu zasu matsa lambar da a aiwatar da kuduri na 1402 an Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, baki dayansa, kuma ba tare da jinkiri ba. Kudurin yayi kiran da a tsagaita wuta, Isra'ila kuma ta janye daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, sannan a koma ga shawarwarin neman zaman lafiya.

Jami'an Turai sun yi kiran da a fadada kokarin shiga tsakani wanda zai kunshi kasashen Turai, da MDD, da kasashen Larabawa masu matsakaicin ra'ayi da kuma ita kanta Amurka.

A halin da ake ciki, fadar White House ta ce shugaba Bush zai yi na'am da komawa ga shawarwarin siyasa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, koda kuwa ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba.

Amma kuma, kakakin fadar White House, Ari Fleischer, ya ce zai yi wuya a samu cimma zaman lafiya idan har aka ci gaba da tashe-tashen hankula.

Har ila yau a jiya larabar, wakilan Falasdinawa a wani taron Kwamitin Sulhun MDD sun bukaci da Isra'ila ta janye cikin gaggawa daga yankunan Falasdinawa. Amma ma'aikatan diflomasiyya sun ce Amurka ta ki yarda ta kara matsin lamba kan Isra'ila.

Jami'ai daga kasar Faransa kuma, suna kiran da a yi tunani sosai kan kafa wata runduna ta kasa da kasa a Gabas ta Tsakiya, wadda zata taimaka wajen aiwatar da kudurorin Kwamitin Sulhu.

XS
SM
MD
LG