Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Canada Ya Gamsu Sosai Da Shirin Raya Kasashen Afirka - 2002-04-08


Firayim Minista Jean Chretien na kasar Canada, ya ce ya gamsu kwarai da ci gaban da ake samu wajen aiwatar da wani shiri na raya kasashen Afirka.

Mr. Chretien yayi wannan furuci nasa jiya lahadi, a bayan da ya gana da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu da sauran shugabannin kasashen yankin a birnin Pretoria.

Mr. Chretien, shugaba mai ci na kungiyar kasashen duniya da suka fi arzikin masana'antu da Rasha, yana ziyarar Afirka domin tattauna Sabon Kawancen Raya Afirka, wanda aka fi sani da sunan "NEPAD" a takaice. Ya ce batun kawancen NEPAD zai zamo daya daga cikin muhimman abubuwan da za a saka cikin ajandar taron kungiyar ta kasashe masu arzikin masana'antu da za a yi cikin watan Yuni, a Kananaskis, Canada.

Firayim ministan na Canada ya ce batutuwa kamar su kare hakkin Bil Adama, dimokuradiyya, gaskiya a mulki tare da yin mulki bisa doka suna daga cikin abubuwan da za a tattauna kai a taron kolin kungiyar tasu.

Kawancen NEPAD ya tsara manufofin habaka mulkin dimokuradiyya da yin mulki tsakani da Allah a Afirka domin samun taimakon tattalin arzikin kasashen yammacin duniya. Kawancen na son ganin an samu bunkasar tattalin arziki da kashi 7 cikin 100 a Afirka daga shekarar 2015.

Daga bisani, Mr. Chretien da Mr. Mbeki sun hadu domin tattaunawa da shugabanni irinsu Festus Mogae na Botswana, da Bakili Muluzu na Malawi, da Joacquim Chissano na Mozambique, da Sam Nujoma na Namibiya, da Benjamin Mkapa na Tanzaniya da kuma mataimakin shugaba Enoch Kavindele na Zambiya.

Ba a gayyaci shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ba, wanda a watan da ya shige ya sake lashen zaben shugaban kasa da ake yin gardama a kai.

XS
SM
MD
LG