Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Ci Gaba Da Yajin Aikin Kin Jinin Gwamnati Har Sai Illa-Ma-Sha-Allahu A Venezuela - 2002-04-11


Kungiyoyin kwadago masu kiyayya da gwamnati a kasar Venezuela, sun lashi takobin ci gaba da yajin aiki har sai illa-ma-sha-Allahu, domin tallafawa ma'aikatan bangaren man fetur na kasar dake tayar da kayar baya.

Masu fashin bakin masana'antun man fetur sun ce wannan yajin aiki zai dora tasiri sosai kan farashin mai a kasuwannin duniya, idan har aka ci gaba da shi na lokaci mai tsawo.

Kasar Venezuela tana cikin Kungiyar Kasashe Masu Sayar Da Man Fetur Ga Sauran Kasashen Duniya, OPEC, kuma ita ce ta hudu cikin jerin masu fitar da mai zuwa wasu kasashen. A kowace rana, Venezuela tana tono fiye da ganga miliyan biyu da dubu 400, inda take sayarwa da Amurka kusan ganga miliyan daya a kowace rana.

Ma'aikatan masana'antun mai na Venezuela suna tsama da shugaba Hugo Chavez kan yadda ake gudanar da kamfanin mai mallakar gwamnatin kasar, "Petroleos de Venezuela."

Masu yin adawa da shugaba Chavez, sun ce wannan yajin aiki da ya shiga rana ta uku da farawa, ya gurgunta ayyuka a matatun man fetur da dama.

Sakataren makamashi na Amurka, Spencer Abraham, ya ce Amurka ta sa idanu sosai kan abubuwan da suke faruwa a kasar Venezuela.

XS
SM
MD
LG