Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Zai Gana Da Sharon Yau Jumma'a... - 2002-04-12


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai gana da firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, nan gaba a yau Jumma'a, a wani bangare na kokarin kawo karshen tashin hankalin dake kara yin muni a Gabas ta Tsakiya.

Sakataren harkokin wajen ya ce wannan tattaunawa zata maida hankali a kan tsarin lokacin janye sojojin Isra'ila daga yankunan Falasdinawa da suka mamaye cikin 'yan kwanakin nan. Isra'ila tayi alkawarin gaggauta janye su, amma kuma har yanzu sojojinta suna cikin manyan biranen Falasdinawa guda hudu.

A gobe asabar kuma, ana sa ran Mr. Powell zai tattauna da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a garin Ramallah wanda ake kaiwa farmaki a Yammacin Kogin Jordan.

Mr. Powell ya isa Isra'ila jiya alhamis daga kasar Jordan, inda ya gana da sarki Abdullahi. Wata sanarwar gwamnatin Jordan ta ce Sarki Abdullahi yayi kira ga Mr. Powell da ya kara matsawa Isra'ila lambar lallai ta janye sojojinta.

Shi kuma sakataren harkokin wajen ya shaidawa 'yan jarida cewa shugaba Bush yana son ya ga an kara samun ci gaba a batun janye sojojin Isra'ila.

XS
SM
MD
LG