Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Chavez Ya Nemi Sasantawa Da Masu Adawa Da Shi A Bayan... - 2002-04-15


Shugaba Hugo Chavez na kasar Venezuela, yayi tayin sasantawa da abokan adawarsa, bayan da ya koma kan karagar mulkinsa cikin nasara, lokacin da juyin mulkin da aka nemi yi masa ya wargaje.

A jiya lahadi, shugaba Chavez ya bada sanarwar cewa yayi na'am da takardar murabus din wakilan hukumar darektocin kamfanin man fetur na kasar mallakar gwamnati, Petroleos de Venezuela, wadanda ya nada a cikin watan Fabrairu. Masu adawa da shi sun yi korafin cewa shugaban yayi wannan nadi ne bisa dalilai na siyasa, ba don dacewa ba.

Wannan sabanin ra'ayi shi ya kai ga mummunar zanga-zangar da aka yi a makon jiya domin goyon bayan ma'aikatan kamfanin man da suka fara yajin aiki suna neman lallai darektocin su yi murabus.

Yajin aikin ya gurgunta ayyukan tono mai a kasar Venezuela, kasa ta hudu cikin jerin masu sayar da man fetur dinsu a kasashen waje.

Majiyoyi sun ce ana ci gaba da kokarin maido da ayyukan tonowa, da tacewa tare da fitar da man kasar zuwa waje kamar yadda aka saba.

A can wani gefen kuma, kasar Cuba, tayi marhabin da komowar shugaba Hugo Chavez kan karagar mulki a Venezuela, kwanaki biyu bayan da aka nemi yi masa juyin mulki.

A jiya lahadi, gidan telebijin na Cuba, yayi ta watsa hotunan komawar shugaba Chavez birnin Caracas, tare da sakonnin bayyana "nasarar juyin juya hali" da kuma na "Allah Ya ja zamanin Hugo Chavez."

Shugaba Fidel Castro na Cuba, yana daya daga cikin manyan aminan shugaba Chavez a yankin yammacin duniya.

Su ma 'yan'uwan Venezuela cikin kungiyar OPEC, Iraq, da Iran da kuma Libya sun yi lale marhabin da komowar shugaba Chavez kan karagar mulki.

Dangantakar shugaba Chavez da kasashen Cuba, da Iran da Iraqi da kuma Libya ta fusata Amurka, wadda take daukar wadannan kasashe hudu a zaman masu goyon bayan ayyukan ta'addanci.

XS
SM
MD
LG