Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Ya Gayyaci Manyan Jami'an Cocin Katolika Na Amurka Zuwa Birnin Rum - 2002-04-16


Paparoma John Paul na biyu ya gayyaci dukkan manyan jami'an Kiristoci mabiya darikar Katolika na Amurka, zuwa wani taron gaggawa a birnin Rum, domin tattauna abubuwan fallasa na yin lalata da yara da ake zargin fada-fada suna aikatawa a majami'un Katolika na nan Amurka.

Fadar paparoma ta Vatican ta ce mai yiwuwa za a yi wannan ganawa a cikin mako mai zuwa. Shugaban Majalisar bishop-bishop ta Cocin Katolika a Amurka, Bishop Wilton Gregory, zai halarci taron na Rum tare da akalla manyan fada masu mukaman Cardinal na Amurka su 8.

Kiran wannan taron gaggawa da fadar Vatican tayi jiya litinin, ya zo 'yan kwanaki kadan a bayan da batun abubuwan fallasar na yin lalata da yara ya buwayi tattaunawar da aka saba yi kowadanne watanni shida tsakanin Paparoma da manyan fadan katolika na Amurka.

Ana zargin cocin na Katolika da laifin yin rufa-rufar danyen aikin da fada-fada ke aikatawa, ta hanyar yi musu sauyin wurin aiki daga wannan gunduma zuwa wancan idan har an zarge su da laifin yin lalatar.

XS
SM
MD
LG