Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Yi Barazanar Auna Shugabannin Isra'ila... - 2002-04-17


Kungiyar Hamas ta mayakan sa kan Falasdinawa, tayi barazanar kashe shugabannin Isra'ila, a saboda kamun da suka yi wa shugaban bangaren kungiyar Fatah, ta Yasser Arafat, Malam Marwan Barghouti.

Isra'ila ta zargi Malam Barghouti da laifin kitsa hare-haren ta'addancin da ake kai mata.

Hamas ta gargadi shugabannin Isra'ila cewa, yanzu su dauki kansu a zaman mutanen da kai musu farmaki ya halalta, suna masu cewa, yanzu kam shugabannin na Isra'ila sun bude kofofin-wuta, ta hanyar damke wannan jami'i na kungiyar Fatah da Isra’ila ta yi.

An kacame da musayar wuta jiya talata a kusa da majami'ar "Nativity" dake birnin Bethlehem, inda tun makonni biyun da suka gabata, dakarun Isra'ila suka yi wa wasu Falasdinawa masu dauke da makamai kofar-rago. Kodayake Falasdinawa sun ce sojojin na Isra'ila, sun kai hari a wannan majami'a, amma sojojin sun musanta haka.

Ta daya gefe kuma, gwamnatin shugaba Bush ta ce, ci gaba da baiwa Falasdinawa agaji daga nan Amurka, zai ta'allaka ne kan nasarar da suka samu a yaki da ta'addanci.

A jiya talata ne, fadar White House ta bada sanarwa gameda wannan sabon sharadi, cikin wata takardar bada izinin ci gaba da bai wa Falasdinawa taimako, watanni shida nan gaba.

Wani jami'in Amurka ya ce, Amurka za ta ci gaba da sa-idanu, walau Falasdinawa za su yi biyayya ga bukace-bukacen Amurkar na ganin an kawo karshen hare-haren kunar-bakin-wake da ake kaiwa Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ambato Sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell, yana cewa, a bana, Amurka ta kudiri bada gudumawar kusan dala milyan 170 ga shirye-shiryen tallafawa Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG