Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Ya Gamsu Da Yadda Isra'ila Take Janyewa... - 2002-04-19


Shugaba Bush ya ce ya gamsu da yadda Isra'ila take janyewa daga yankin Yammacin kogin Jordan, yana mai fadin cewa zai sa idanu ya ga ko shugaban Falasdinawa zai cika alkawarin da yayi na yakar ta'addanci.

Mr. Bush ya fadawa 'yan jarida jiya alhamis a fadar White House cewar firayim ministan Isra'ila Ariel Sharon, yana aiki sosai da tsarin lokacin da ya bayar na janyewa daga yankin Yammacin kogin Jordan.

Mr. Bush ya ce yayi imani cewar Mr. Sharon mutum ne mai son zaman lafiya.

Babban jami'in shawarwari na Falasdinawa, Saeb Erekat, ya mayar da martani a fusace kan wannan furuci na shugaba Bush. A cikin hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, Malam Erekat ya ce Mr. Bush yana jinjinawa ayyukan ta'addanci ne da gwamnatin wata kasa, watau Isra'ila take aikatawa. Ya ce wannan furuci ya nuna a fili cewar Amurka ta fi kaunar Isra'ila.

Sakataren harkokin waje, Colin Powell, ya bayyanawa shugaba Bush sakamakon rangadin kwanaki 10 da yayi a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya kasa cimma tsagaita wutar da aka yi fata a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG