Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Limaman Cocin Roman Katolika Na Amurka Suna Birnin Rum... - 2002-04-23


Yau talata manyan limaman cocin kiristoci 'yan darikar Roman Katolika na Amurka, zasu fara tattaunawa a fadar Paparoma ta Vatican, da nufin akwo karshen rikicin da ya goce cikin wannan darika a Amurka, bisa zarge-zargen cewa wasu fada suna yin lalata da yara kanana.

An shirya manyan limaman masu mukaman "Cardinal" zasu gana cikin sirri da Paparoma John Paul jiya litinin, kafin taron kolin kwanaki biyu da zasu fara yau talata.

Ana zargin babban limamin cocin Roman Katolika na gundumar Boston, Cardinal Bernard Law, da laifin yin canjin wurin aiki da gangan ma limaman da aka tuhuma da laifin yin lalata da yara, maimakon tube su daga kan mukamansu.

Amurkawa 'yan darikar Roman Katolika da dama da suka fusata, sun bukaci da yayi murabus shi kansa.

Jaridar Los Angeles Times ta ce da yawa daga cikin limaman cocin na Amurka da suka je ganawa da Paparoma, zasu roki fadar Vatican da ta bukaci Cardinal Law yayi murabus.

XS
SM
MD
LG