Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Kasar Nepal Sun Tada Bam A Hasumiyar Filin Jirgin Sama - 2002-04-30


'Yan tawaye masu akidar Mao a Nepal sun tayar da bam a hasumiyar wani filin jirgin sama dake karkara, suka gurgunta zirga-zirgar jiragen sama a gundumar Khotang a gabashin kasar.

Wani jami'in kula da zirga-zirgar jiragen saman fararen hula ya ce harin bam din na jiya litinin ya ragargaza hasumiyar kula da sauka da tashin jirage a filin jirgin saman Lamidada, amma kuma babu wani wanda ya ji rauni.

Wannan harin ya biyo bayan sanarwar da jami'an Nepal suka bayar cewa an kashe 'yan tawaye kimanin 30 cikin 'yan kwanaki kadan da suka shige a farmaki na baya-bayan nan da gwamnati ta kaddamar.

'Yan sanda sun ce da yawa daga cikin 'yan tawayen sun mutu a kazamin fadan da aka gwabza a lokacin da sojoji suka kai hari kan sansanonin horas da 'yan tawayen da kuma tungayensu cikin tsaunukan dake lungun kasar.

An kashe mutane fiye da dubu 3 a Nepal tun daga lokacin da 'yan tawayen masu akidar Mao (Tse Tung, tsohon shugaban China) suka fara kai farmaki shekaru shida da suka shige domin maye gurbin mulki irin na sarauta a kasar da tsarinsu na Kwaminisanci.

XS
SM
MD
LG