Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiyar Musulmi Ta Ce Kai Farmaki A Kan Musulmi Na Karuwa A Amurka - 2002-05-01


Wata kungiyar Musulmi ta ce rahotannin nuna kyama ga Musulmi a nan Amurka, da suka hada har da tozarta su, da nuna masu bambanci, da ma na kisa, sun rubanya har sau uku cikin shekara guda da ta gabata.

Wannan kungiyar da hedkwatarta ke nan birnin Washington, da aka fi sani da sunan Majalisar Huldar Musulmin Amurka da sauran bangarori, ko kuma CAIR a takaice, ta fada jiya talata cikin wani rahoto cewa, hukumomi sun samu rahotanni fiye da dubu daya da 500 masu nasaba da irin takurawar da aka yi wa musulmi cikin shekara guda--ma'ana zuwa karshen watan jiya na maris. Kungiyar ta ce, irin wadannan matsaloli sun fi ta'azzara, jim-kadan bayan harin ta'addanci na 11 ga watan satumbar bara.

Kungiyar ta CAIR ta ce, manufofin da gwamnatin Amurka ta zartar bayan wannan hari, sun yi bahagon tasiri ga wasu musulmi su dubu 60, ciki har da wasu su dubu da dari biyu da ake tsare da su saboda matsaloli masu nasaba da dokokin shiga-da-fita Amurka.

Kungiyar musulmin ta ce, an dauki irin wadannan mutane da aka tsare tamkar 'yan ta'adda, yayin da kuma wadanda suke da takardun halas na zama Amurkar aka umurce su da su kai kansu ga hukuma bisa ganin dama, domin su amsa wasu tambayoyi.

Ko da yake tuni shugaba Bush da atoni-janar John Ashcroft suka ce ba za a amince da tabi'ar nuna wa musulmi bambamci ba, amma har yanzu ma'aikatar shari'ar Amurkar ba ta mayar da martani ga wannan sabon rahota ba.

Babban daraktan kungiyar, ko kuma majalisar musulmin Amurkar ta CAIR, Nihad Awad, ya ce musulmin kasar nan suna goyon bayan manufofin gwamnati na kyautata matakan tsaro, yana mai nunin cewa, akwai musulmi cikin wadanda aka kashe, lokacin da suke gwagwarmayar ceton rayuka a ranar 11 ga watan na satumba. Amma Malam Awad ya yi nunin cewa, bambamce-bambamcen kabila dana addini suna bada wata irin bahaguwar fassara ga abinda ake nufi da harkokin tsaro.

XS
SM
MD
LG