Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Ya Ce Za A Gudanar Da Taron Neman Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya - 2002-05-03


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce ana kan shirye-shiryen gudanar da taron neman zaman lafiya na kasa da kasa kan Gabas ta Tsakiya domin samar da hanyar sulhunta rikicin Isra'ila da Falasdinawa, tare da kirkiro kasar Falasdinu.

Sakatare Powell ya bada sanarwar shirye-shiryen jiya alhamis a Washington, a bayan da ya gana da jami'ai daga Rasha, da Kungiyar Tarayyar Turai, da Majalisar Dinkin Duniya, wadanda zasu taru su hada karfi wuri guda domin shirya kokarin na samar da zaman lafiya.

Har yanzu ba a tsayar da wuri, ko lokaci da kuma wadanda zasu halarci taron ba, amma Mr. Powell ya ce ana iya farawa nan da 'yan watanni kadan. Ya ce zasu takali batutuwan jinkai, da kuma batutuwan tsaro da sauye-sauyen tattalin arziki, yayin da zasu nemi hanyoyin siyasa na kafa kasar Falasdinu.

Shugaba Bush ya ce tilas a kai ga cimma kafuwar kasar Falasdinu ta hanyar tattaunawa tare da kawo akrshen mamayar da Isra'ila tayi wa yankunan Falasdinawa, kuma tilas ne sabuwar kasar da za a kafa ta rungumi dimokuradiyya.

XS
SM
MD
LG