Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon Ya Ce Isra'ila Ba Zata Mika Kai Ga Masu Neman Durkusar Da Ita Ba - 2002-05-08


Firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila, ya bayyana harin kunar-bakin-wake da aka kai jiya talata kusa da birnin Tel Aviv, a zaman alamar "aniyar gaskiya" ta Malam Yasser Arafat, game da kasar Isra'ila.

Kafin ya tashi zuwa gida Isra'ila, Mr. Sharon ya shaidawa 'yan jarida cewa Isra'ila zata dauki kwararan matakai kan wadanda suka kai mata hari, kuma ba zata mika wuya ga abinda ya kira neman yi mata kusa ba.

Mr. Sharon ya katse ziyarar da ya kawo nan birnin Washington a bayan harin.

Shugaba Bush ya bayyana kyamarsa ga "daukar rayukan mutanen da ba su san fari ba, balle baki" da aka yi a wannan harin bam. Shugaban ya shafe fiye da sa'a guda yana tattauna rikicin Isra'ila da Falasdinawa da Mr. Sharon a fadar White House jiya talata.

Daga baya, Mr. Bush ya sake jaddada goyon bayan Amurka ga kafa kasar Falasdinu. Amma kuma Mr. Sharon ya ce riga-malam-zuwa-masallaci a yi wannan magana a yanzu, har sai majalisar mulkin kai ta Falasdinawa ta gudanar da sauye-sauye.

XS
SM
MD
LG