Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sabon Nazari Ya Gaskata Ikirarin Cewa Jariran Da Suka Sha Nonon Uwa, Sun Fi Basira - 2002-05-09


Wani sabon nazarin da aka gudanar ya ce jariran da suka sha nonon uwa na watanni tara, sukan girma cikin koshin lafiya tare da nuna basira fiye da jariran da suka sha nonon wata daya ko kasa da haka.

Wannan nazari, wanda Mujallar Kungiyar Likitocin Amurka, JAMA, ta buga, ya gaskata ayyukan bincike-binciken da aka gudanar a can baya, wadanda suka tabbatar da fa'idar shan nonon uwa.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa nonon uwa, yana samar da sigogin abinci, da kuma kariya fiye da komai ga jariri, sannan kuma yana sanya jariri ya tashi da basira.

Wannan nazarin ya shafi samari maza da mata su fiye da dubu uku, wadanda aka yi nazarinsu a Copenhagen, a kasar Denmark.

Har ila yau kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ambaci wani nazarin dabam, wanda makarantar nazarin aikin likita ta Davis a Jami'ar California ta gudanar, wanda shi ma ke nuna fa'idar nonon uwa ga jarirai.

XS
SM
MD
LG