Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Da Sarki Abdullahi Na Jordan Sun Tattauna A Fadar White House - 2002-05-09


Shugaba Bush da Sarki Abdullahi na Jordan sun gana a fadar White House domin tattauna kokarin wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Kafin su fara tattaunawar tasu ta jiya laraba, Mr. Bush ya shaidawa 'yan jarida cewa yana fata firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila zai tuna da yadda za a bi a samu zaman lafiya, a yayin da yake auna irin martanin da Isra'ila zata maida game da harin kunar-bakin-wake na Falasdinawa na ranar talata.

Har ila yau, Mr. Bush ya ce, "babbar alamar karfafa guiwa" ce umurnin da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, ya bai wa jami'an tsaronsa na su dakile hare-haren da ake kaiwa kan fararen hula 'yan Isra'ila.

Sarki Abdullahi na Jordan, ya ce ministan harkokin wajen kasarsa zai tuntubi sauran shugabannin kasashen larabawa, domin tsara abinda ya kira akidar da aka tsaida a Beirut.

Taron kolin kasashen larabawa na bana da aka yi a birnin Beirut, ya amince da wani shirin zaman lafiyar da kasar Sa'udiyya ta gabatar, wanda a karkashinsa dukkan kasashen larabawa zasu kulla huldar zumunci da Isra'ila idan har ta janye daga dukkan yankunan larabawa da ta mamaye a yakin Gabas ta Tsakiya na 1967.

XS
SM
MD
LG