Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Jefa Kuri'a Kalilan Suka Fito Domin Zabe A Kasar Mali - 2002-05-13


'Yan kallo sun bada labarin cewa mutane kalilan ne suka fito domin jefa kuri'unsu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Mali da aka kammala jiya lahadi.

An gwabza a karon na biyu a tsakanin tsohon shugaban gwamnatin soja, Janar Amadou Toumani Toure, da Soumaila Cisse, dan takarar jam'iyyar dake mulkin kasar. Gwamnati ta ce ba zata fara bayyana sakamakon zaben ba har sai an kidaya akalla rabin kuri'un da aka kada.

Kuri'ar da aka jefa, ita ce zata fitar da magajin shugaba Alpha Oumar Konare mai barin gado, wanda ya kammala shugabancinsa kamar yadda tsarin mulki yayi tanadi.

A farkon mako kotun tsarin mulki ta Mali ta bada sanarwar cewa Malam Toure da Malam Cisse ne zasu gwabza a zagaye na biyu.

XS
SM
MD
LG