Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarki Abdullahi Na Jordan Ya Ce Shirin Samar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya Ya Wargaje - 2002-05-14


Sarki Abdullahi an Jordan ya ce ba wai lalacewa shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya yayi ba, ya wargaje ne baki daya, inda ya haifar da barna mai dimbin yawa.

A lokacin da yake magana jiya litinin a Washington, sarkin ya ce ana bukatar jagorancin Amurka domin tsamo yankin daga bala'in da take dab da fadawa ciki.

Yayi kiran da a gudanar da sabbin shawarwarin gaggawa wanda za a fara da bayyana burin da kowane bangare ke da nufin cimmawa.

Sarkin na Jordan ya ce babu ta yadda za a tsammaci Falasdinawa su kawo karshen ta'addanci ko kuma su koma ga tattaunawa da Isra'ila ba tare da alkawarin cewa zasu samu kasarsu ta kansu ba. Har ila yau ya ta yaya ne Falasdinawa ko Larabawa zasu dakile ayyukan ta'addanci, idan har babu wani abin alherin da suke hange.

Sarkin ya ce haka kuma wannan ma ya shafi 'yan Isra'ila, wadanda ya ce ba zasu yi kokarin yin azaman tare ko kuma yarda da muradun Falasdinawa ba, har sai an tabbatar musu da tsaro, kana Larabawa suka yi na'am da su.

XS
SM
MD
LG