Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin Amurka Ya Gabatar Da Shawara Kan Cimma Zaman Lafiya A Sudan - 2002-05-15


Wakilin Amurka na musamman a kasar Sudan, John Danforth, ya ce ya kamata Amurka ta taimaka wajen tabbatar da wanzuwar kokarin da ake yi yanzu na kawo karshen yakin basasar da aka jima ana yi a kasar Sudan.

John Danforth ya gabatar da wannan shawara cikin wani rahoton da fadar shugaban Amurka ta White House ta bayar jiya talata. Shawarar ta ce bai kamata Amurka ta kaddamar da wani sabon yunkuri wanzar da zaman lafiya a Sudan ba, kamata yayi tayi kokarin ganin an cimma zaman lafiya a kokarin yin sulhun da kasar Kenya ke jagoranci. Har Ila yau, Mr. Danforth ya ce ya kamata Amurka ta dora muhimmanci sosai kan ayyukan agajin jinkai.

A watan satumbar bara ne Mr. Bush ya nada Mr. Danforth a zaman wakilinsa na musamman a Sudan. Yayi rangadin Sudan da yankin a watannin Nuwamba da Janairun da suka shige.

Mutane fiye da miliyan biyu suka mutu a yakin basasar Sudan, wanda Mr. Danforth ya ce babu wani bangaren da zai lashe shi a fagen daga.

XS
SM
MD
LG