Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuri'ar Neman Ra'ayoyin Jama'a Ta Nuna Cewa Mafi Yawan 'Yan Isra'ila Zasu Yarda Da Kafa Kasar Falasdinu - 2002-05-15


Wata sabuwar kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a da aka yi a Isra'ila, ta nuna cewa kusan kashi biyu cikin uku na wadanda aka tambaya sun ce zasu yarda da kafa kasar Falasdinu a cikin kammalalliyar yarjejeniyar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Wannan kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a wadda jaridar "Yediot Aharonot" ta gudanar, ta zo kwanaki biyu kawai a bayan da jam'iyyar Likud mai mulkin Isra'ila ta zartas da wani kudurin da ya ki yarda da kafa kasa ta Falasdinawa.

Firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya fadawa majalisar dokoki a jiya talata cewa zai koma ga shawarwarin da zasu kai ga kafa kasar Falasdinu, idan har majalisar mulkin kai ta Falasdinawa ta gudanar da garambawul kan yadda take gudanar da ayyukanta, sannan kuma ta kawo karshen hare-haren da ake kai wa Isra'ila.

Watakila shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, zai takali wannan batu na yin garambawul a yau laraba, a lokacin da zai yi jawabi ga majalisar dokokin Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG