Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun MDD Ya Sake Fasalin Takunkumin Iraqi - 2002-05-15


Ba tare da wata hamayya ba, Kwamitin Sulhun MDD ya amince da yin garambawul sosai ga fasalin takunkumin da ake yin aiki da shi a kan kasar Iraqi.

Kwamitin sulhun mai wakilcin kasashe 15 ya zartas da wannan kudurin jiya talata, inda ana dab da jefa kuri'ar kasar Syria ta canja ra'ayi ta ce zata goyi bayan sabon fasalin takunkumin.

Sabon takunkumin ya kara tsaurin sayen kayayyakin da gwamnatin Iraqi zata iya amfani da su a fagen ayyukan soja, yayin da ya saukaka shigar kayayyakin da fararen hula ne kawai zasu iya amfani da su.

Wani kakakin fadar shugaban Amurka ta White House, ya yaba da takunkumin da aka yi masa garambawul din, a zaman matakin ci gaba ga al'ummar Iraqi.

Amma kuma jakadan Iraqi a MDD, Mohammed al-Douri, ya ce hukumomi a birnin Bagadaza, ba su ji dadin wannan kuri'a ba, yana mai fadin cewa jerin kayayyakin da sai an bada Iraqi izni kafin ta saya, zai nakkasa tattalin arzikin kasar.

XS
SM
MD
LG