Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indiya Ta Kara Girka Sojoji Cikin Damara A Kashmir - 2002-05-20


Indiya ta kara girka sojojinta a yankin nan na Kashmir da ake tabka rikici kansa, a yayin da ministan harkokin waje Jaswant Singh yake jan kunnen Pakistan da cewa Indiya zata dauki fansar duk wani sabon harin da za a kai mata daga tsallaken kan iyaka.

A jiya lahadi, majalisar zartaswar tsaro ta Firayim minista Atal Behari Vajpayee, ta bada umurnin cewa dukkan rundunonin jami'an dake dauke da makamai a kasar Indiya zasu koma karkashin ikon rundunar sojojin kasar kai tsaye, yayin da dogarawan tsaron bakin tekun kasar zasu koma karkashin kulawar rundunar sojojin ruwa.

Wannan shawara ta biyo bayan wani mummunan harin da aka kai kan wani sansanin jami'an tsaron Indiya cikin dare, harin da ake kyautata zaton wasu masu kishin Islama ne suka kai a arewa maso gabas da Jammu, da kuma irin musanyar wutar da ake yi babu tsaitsayawa a rana ta uku a jere a bakin layin nan da ya raba Kashmir gida biyu.

Pakistan dai ta ce babu ruwanta da harin da aka kai kan Indiya, tana mai cewa ta haramta kungiyoyin 'yan kishin Kashmir masu zazzafan ra'ayi, ta kuma ce zata yi kokarin warware sabanin dake tsakaninta da Indiya ta hanyar lumana.

XS
SM
MD
LG