Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Shirin Yin Amfani Da Na'urar Tantance Karya Da Gaskiya... - 2002-05-21


Gwamnatin Amurka zata fara gwaje-gwaje da na'urar tantance karya da gaskiya a wasu cibiyoyin gwamnatin tarayya biyu, domin gano ko wani ma'aikacin wurin ne yake da alhakin kai hare-hare da kwayoyin cutar Anthrax cikin wasiku a shekarar da ta shige.

Jami'ai sun ce a cikin wata mai zuwa na Yuni, ma'aikatar shari'a zata fara daura wa daruruwan ma'aikata na'urar ta tantance karya da gaskiya, tana yi musu tambayoyi a sansanin soja na Fort Detrick dake Jihar Maryland, da kuma Makarantar sojoji ta Dugway Proving Ground dake Jihar Utah. Ana adana kwayoyin cutar Anthrax a wadannan cibiyoyin biyu.

Gidan telebijin na ABC ya ce wadannan gwaje-gwaje zasu hada har da tsoffin ma'aikatan cibiyoyin biyu.

Jami'ai suka ce gwamnati zata fi maida hankali a kan ma'aikatan da suke iya shiga inda ake ajiye kwayar cutar ta Anthrax, suke kuma da kwarewa wajen harhada makami da wannan kwayar cuta.

Binciken kimiyya da aka gudanar na kwayar cutar Anthrax da ta kashe mutane biyar a shekarar da ta shige, ya nuna cewa jinsinta yayi kama da jinsin Anthrax mai suna "Ames" wanda ake adanawa a sansanin sojojin Amurka na Fort Detrick.

Tun lokacin da aka kai hare-haren, an yi ta samun rahotannin rashin kyakkyawan tsaro a Fort Detrick, inda nan ne Cibiyar Binciken Cututtuka Masu Yaduwa ta Rundunar Sojojin Amurka take.

XS
SM
MD
LG