Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Makoki A Kasar Mozambique - 2002-05-27


Al'ummar Mozambique suna jimamin mutuwar mutane kusan 200, wadanda suka halaka a hadarin jirgin kasar da aka ce yana daya daga cikin mafiya muni a tarihin kasar.

Wasu daruruwan mutanen sun ji rauni a wannan hadari, wanda ya faru ranar asabar a garin Moamba, mai tazarar kilomita 40 a yamma da Maputo, babban birnin kasar. Jami'ai suka ce a jiya lahadi aka fara binne wasu daga cikin wadanda suka mutu.

A jiya lahadi shugaba Joacquim Chissano ya ziyarci inda hadarin ya faru, ya kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku. Ya bayyana hadarin jirgin kasar a zaman bala'in da ya shafi kasa baki daya, ya kuma yi kira ga al'ummar kasar da su bada gudumawar jini, su kuma nuna cikakken goyon bayansu ga wadanda hadarin ya shafa.

Jami'ai suka ce yawan wadanda suka mutu da wadanda suka ji rauni yana son ya fi karfin asibitocin Mozambique, wadanda tuni suka fara karancin magunguna da kayan aiki a saboda barkewar annobar zazzabin cizon sauro da kwalara a farkon shekarar nan.

Wannan jirgin kasa, wanda ke jan taragai na fasinja da kuma na kayayyaki, yana kan babban layin dogon da ya hada Mozambique ad Afirka ta Kudu ne.

Rahotanni sun ce direban jirgin kasar, ya cire taragan da suke dauke da kayayyaki daga jikin jirgin, a bayan da shi wannan jirgi ya cije ya kasa tafiya gaba a lokacin hawa wani tudu. Daga nan sai aka yi amfani da manyan duwatsu domin a yi waijin taragan da suke dauke da fasinjoji.

Amma kuma, sai duwatsun da aka yi waiji da su suka kauce, sai taragan dake dauke da fasinjojin suka yiwo baya da gudu, suka ci karo da wani taragu dake tsaye a cike da siminti.

XS
SM
MD
LG