Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya Ta Musanta Rahoton Tayin Bada Diyya Ga Iyalan Mamatan Lockerbie - 2002-05-30


Libya ta musanta rahotannin da aka bayar cewa ta gabatar da tayin biyan diyyar dala miliyan dubu biyu da dari bakwai ga iyalan wadanda suka mutu a lokacin da bam ya tashi ya tarwatsa jirgin saman kamfanin Pan Ama Lockerbie, a kasar Scotland a shekarar 1988.

A cikin wata sanarwar hukuma, wani kakakin gwamnatin Libya ya ce lallai wasu 'yan kasuwar Libya sun gana da iyalan mamatan, amma kuma ba a shaidawa gwamnati sakamakon tattaunawarsu ba.

A ranar talata ne wasu lauyoyin birnin New York dake wakiltar iyalan a tattaunawa da gwamnatin Libya, suka bada sanarwar wannan tayin. Suka ce biyan diyyar zai dogara a kan dage takunkumin MDD da na Amurka a kan Libya.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce biyan diyyar, idan har da gaske ne, mataki ne da ya dace. Amma kuma ya ce biyan diyya ba zai warware dukkan batutuwan dake tattare da Libya da kuma bam din da aka dasa cikin jirgin na kamfanin Pan Am mai lambar tafiya 103 ba.

XS
SM
MD
LG