Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Kasar Philippines Sun Fara Nuna Damuwar Yin Atusaye Da Sojojin Amurka - 2002-06-04


Wasu 'yan majalisar dokokin kasar Philippines, sun fara nuna damuwa kan wata shawarar girka sojojin Amurka a kusa da bakin daga, inda dakarun kasar ke yakar Musulmi 'yan aware.

Shugaban kwamitin hulda da kasashen waje a majalisar wakilan Philippines, Apolinario LOzada, ya shaidawa Muryar Amurka cewa kyale sojojin Amurka suna yin rakiya ma sojojin Philippines a lokacin ayyukan sintiri, zai iya haddasa matsaloli.

Tsarin mulkin kasar Philippines, ya haramtawa sojojin kasashen waje shiga cikin duk wata gwabzawa a fadin yankin kasar.

Mukaddashin sakataren tsaron Amurka dake ziyara a kasar, Paul Wolfowitz, ya ce sojojin na Amurka ba zasu shiga cikin wata gwabzawa ba. Ya ce aikinsu shine horas da sojojin Philippines ta yadda zasu iya yakar 'yan tawayen Abu Sayyaf, wadanda Amurka ta ce suna da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta al-Qa'ida.

Shugabar Philippines, Gloria Arroyo, ta ce tana goyon bayan ra'ayin tura sojojin Amurka bakin daga tare da kananan bataliyoyin sojan Philippines.

XS
SM
MD
LG