Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abokan Adawar Siyasa Na Madagascar Zasu Gana A Senegal - 2002-06-06


Abokan adawar siyasa na Madagascar sun yarda zasu gana a wani wurin nesa da inda suke rikici a karo na biyu, domin suyi kokarin warwarefitinar da ta kaure a wannan tsibiri nasu.

Ministan harkokin wajen Senegal, Cheikh Tidiane Gadio, ya shaidawa Muryar Amurka cewa mutumin da ya jima yana mulkin kasar Madagascar, Didier Ratsiraka, da sabon shugaban da aka rantsar a kasar, Marc Ravalomanana, sun ce zasu gana ranar asabar a Dakar, babban birnin Senegal.

Mr. Gadio ya ce wannan tattaunawa, wadda Kungiyar Hada kan Kasashen Afirka ta OAU zata dauki nauyin gudanarwa, zata hada da shugabannin Afirka da dama.

Mr. Ratsiraka da Mr. Ravalomanana sun gana a birnin na Dakar cikin watan Afrilu a bayan da rikicin zabe ya kaure tsakaninsu, inda suka yarda da a sake kidaya kuri'u. Mr. Ratsiraka ya ki yarda da sakamakon sake kidaya kuri'un, a bayan da ya bayyana cewa Mr. Ravalomanana ne ya lashe zaben kai tsaye.

XS
SM
MD
LG