Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Baitulmalin Amurka Ya Ce Ziyarar Da Ya Kai Afirka Zata Taimaka Wajen Tsara Manufar Agajin Tattalin Arziki - 2002-06-06


Sakataren baitulmalin Amurka, Paul O'Neill, wanda ya komo daga Afirka, ya ce rangadin da ya kai nahiyar zai taimaka wajen tsara manufofin bada agajin raya kasa ga nahiyar.

A cikin jawabin da yayi a jami'ar Georgetown dake nan cikin birnin Washington a jiya laraba, Sakatare O'Neill ya ce shirye-shiryen bada agaji suna yin aiki, to amma kuma bunkasar dogon lokaci a nahiyar Afirka zai dogara ne kan basirar kasuwanci na 'yan Afirka, da cinikayya da kuma zuba jarin kasashen waje.

A lokacin wannan rangadin kwanaki goma da ya kai tare da mawakin zamani dan kasar Ireland, Bono na kungiyar U-2, Mr. O'Neill ya ziyarci Ghana da Uganda, da Afirka ta Kudu da kuma Ethiopia.

Mr. O'Neill ya ce ya ga fannoni uku na jarurruka masu nagarta a nahiyar Afirka: ruwan sha mai kyau, da bayar da ilmin firamare, da kuma yaki da kwayar halittar cuta ta HIV mai haddasa kanjamau, ko AIDS ko kuma SIDA.

Ya ce Amurka zata bada karin agajin tattalin arziki ga kasashen da suke mulkin dimokuradiyya, suke kuma da gwamnatoci masu kamanta gaskiya.

XS
SM
MD
LG