Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Abka Cikin Hedkwatar Malam Arafat, Amma Suka Janye Daga Baya - 2002-06-06


Sojojin Isra'ila sun janye daga cikin hedkwatar shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a garin Ramallah, bayan da suka kutsa ciki yau da asubahi tun kafin ketowar alfijir.

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce tankoki da sojoji sun janye daga kewayen hedkwatar Malam Arafat a yankin Yammacin kogin Jordan.

Majiyoyin tsaron Falasdinawa sun ce da asubahin yau alhamis ne tankokin yakin Isra'ila da motoci masu sulke suka shiga wannan birni dake yankin Yammacin kogin Jordan, kuma nan take suka kewaye ginin hedkwatar Malam Arafat, suka kutsa ciki.

Majiyoyin suka ce wutar da tankokin Isra'ila suka yi ta budewa, ta kashe Bafalasdine daya, ta raunata wasu shida. An lalata wasu gine-ginen da dama.

Amma kuma jami'an Falasdinawa sun ce babu abinda ya taba lafiyar Malam Arafat. Isra'ila ma ta ce sojojinta ba su da niyyar taba lafiyar shugaban na Falasdinawa.

Wannan farmaki ya biyo bayan wani harin bam na Falasdinawa kan wata motar safar Isra'ila, wanda ya kashe mutane 17 ya raunata wasu 40. 13 daga cikin wadanda suka mutun sojojin Isra'ila ne.

Kungiyar kishin Falasdinu ta "Islamic Jihad" ta dauki alhakin kai harin, tana mai bayyana maharin da cewa dan shekaru goma sha wani abu ne daga garin Jenin. Majalisar mulkin kai ta Falasdinawa tayi tur da harin tana mai cewa tana farautar masu zazzafan ra'ayin da suka tura wannan dan harin bakin wake.

XS
SM
MD
LG