Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Laraba Za A Sake Samun Masu Shiga Zagaye Na Biyu A Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya - 2002-06-12


Tunanin wucewa zuwa ga zagaye na biyu a gasar cin kofin kwallon kafar duniya zai yi daram a zuciyar 'yan wasa da 'yan kallo yau laraba a lokacin da Ingila zata kara da Nijeriya, yayin da ita kuma Ajantina zata kara da Sweden a Japan.

Ingila ita ce ta biyu a wannan rukuni nasu na shida ko "F" da maki hudu, a bayan kasar Sweden wadda ita ma maki hudu gare ta, sai dai ta jefa kwallaye fiye ad Ingila.

Ajantina ita ce ta uku, amma kuma tana iya hayewa zuwa gaba. Nijeriya dai tuni an yi waje da ita, aka nunawa 'yan wasanta hanyar komawa Lagos. Ajantina tana bukatar lashe wasan yau, ko kuma sai Nijeriya ta lallasa Ingila kafin ita Ajantinar ta zarce.

A rukuni na biyu ko "B" kuma, Spain zata kara da Afirka ta Kudu, yayin da Slovenia zata kara da Paraguay. Spain dai ta riga ta samu matsuguni a zagaye na biyu. A yanzu haka, Afirka ta Kudu ita ce ta biyu a wannan rukuni, sai Paraguay wadda take ta uku. Slovenia ma dai ta 'yan Super eagles aka yi mata, babu inda zata dosa daga yau im ba gida ba.

A wasannin da aka gwabza jiya talata, Senegal ma-ba-da-mamaki da Jamus, ad Ireland, da Denmark duk sun samu zarcewa zuwa zagaye na biyu a gasar da ake yi a Japan da Koriya ta Kudu.

An yi waje-rod da kasar Faransa mai rike da kofin kafin jiya, a bayan da Denmark ta birkice ta da ci 2 da babu. Kasar Kamaru ma ba ta ji dadin wasa jiya talata ba, a bayan da Jamusawa suka banke ta da ci 2 da babu. jamus ad Ireland sun zarce a wannan rukuni, yayin ad 'yan Kamaru suak doshi birnin Yaounde, 'yan Saudi Arabiya kuma suka doshi Riyadh.

XS
SM
MD
LG