Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Lahadi 'Yan Kamaru Zasu Yi Zaben 'Yan Majalisar Dokoki - 2002-06-23


Masu jefa kuri'a na kasar Kamaru, zasu zabi sabuwar majalisar dokoki tare da majalisun kananan hukumomi yau lahadi, a zaben da ake kyautata zaton cewa jam'iyyar shugaba Paul Biya mai mulkin kasar ce zata lashe.

A yanzu haka dai, jam'iyyar "Democratic Rally of the Cameroonian People" ta shugaba Paul Biya, tana da kujeru 116 cikin majalisar dokokin, yayin da babbar jam'iyyar adawa ta "Social Democratic Front" take da kujeru 43.

Shugaban adawa, John Fru Ndi, ya zargi hukumar zaben kasar da laifin nuna fifiko ga jam'iyyar da take mulki, ta hanyar kin yin rajistar 'yan takara masu yawa na 'yan adawa a cikin zaben majalisar dokoki.

A zaben 1997 ma, jam'iyyar ta Social Democratic Front ta zargi magoya bayan Mr. Biya da yin magudi, ta kuma bukaci da a soke sakamakon zaben.

XS
SM
MD
LG