Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sa'udiyya Ta Ce Falasdinawa Ne Kadai Zasu Iya Zaben Shugabanninsu - 2002-06-27


Kasar Sa'udiyya ta ce, Falasdinawa ne kadai, za su iya zaben shugabanninsu.

Wannan furuci na Sa'udiya ya nisantar da kasar daga matsayin shugaban Amurka, George Bush, wanda ya yi kiran samar da sabbin shugabanni wadanda ba sa lamuntar ayyukan ta'addanci ga Falasdinawa.

Ministan harkokin wajen Sa'udiyya, Sa'ud al-Faisal, ya ce, ya wajaba sauran kasashen duniya su yi na'am da dukkan mutumin da Falasdinawa suka zaba a matsayin jagoransu.

Tun farko a jiya laraba, sai da wani babban kakakin Falasdinawa ya ce, Malam Yasser Arafat zai nemi a sake zabarsa a kuri'ar da za a kada cikin watan Janairun badi.

A nan Washinton kuwa, wani kakaki a ma'aikatar harkokin wajen Amurka cewa ya yi, sake zabar Malam Arafat zai sake mayar da Falasdinawa ga abinda ya kira "wata hanya marar makura."

XS
SM
MD
LG